News
Matatar man Dangote Ta Maka Hukumar NMDPRA A Gaban Kotu
Matatar man Ɗangote ta shigar da antoni-janar na ƙasa ƙara tana neman a janye dukkan lasisin shigo da man fetur da aka bai wa dillalan man fetur da kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC).
Wannan ƙara ta sake tada tsattsamar alaƙar da ke tsakanin matatar da hukumar kula da albarkatun man fetur ta ƙasa bayan janye makamanciyar wannan ƙara da matatar ta yi a baya inda ta ƙalubalanci izinin shigo da man fetur da aka bai wa NNPC da wasu ‘yan kasuwa masu shigo da mai daga waje.
Rikicin KCSF: An Bukaci Hadin Kan Ƙungiyoyi Domin Kare Manufofin “Kano First”
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Dangote ya shigar da ƙarar ce a gaban babbar kotun tarayya da ke jihar Legas inda yake neman kotun da ta soke sabunta lasisin da hukumar kula da albarkatun man fetur ta ƙasa (NMDPRA) ta yi.
Dangote ya ce ba da lasisin ya saɓa wa umarnin kotu ta bayar a farko inda ta buƙaci dukkan ɓangarorin su koma matakin baya da ake kai.
Mun buƙaci ƙarin bayani game da sabuwar ƙarar daga wajen jami’in sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, sai dai bai samu yi mana ƙarin bayani ba a lokacin da muke haɗa wannan rahoton.
A cikin ƙarar, matatar ta ce lasisin da aka bai wa wasu ‘yan kasuwa a wannan wata barazana ce ga ayyukanta kuma ya saɓa wa tanadi na doka wanda ya ce za a ba da lasisin shigo da mai ne kaɗai idan ya zama man da ake samarwa a cikin gida ba zai iya wadatar da ƙasar ba.
Hukumar NMDPRA har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamari ba. sai dai wani jami’i daga sashen hulɗa da jama’a na hukumar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana da manema labarai, ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Asabar cewa hukumar ba ta da masaniya kan shigar da ita ƙara.
Mahukunta da dillalan man fetur sun sha ba da hujjoji kan shigo da mai daga waje, suna masu cewa har yanzu suna da rawar da za su taka domin tabbatar da cewa samar da man fetur da magance ƙarancinsa musamman kasancewar a yanzu ne matatar cikin gida ke daɗa bunƙasa.
Game da abin da ya faru a baya:
Tun bayan fara gudanar da ayyukanta a shekarar 2024, matatar man Dangote na ta ƙoƙarin ganin ‘yan kasuwar cikin gida sun sayi man fetur daga matatun cikin gida a maimakon shigo da mai daga waje.
Sai dai tsohon shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, ya sha ƙalubalantar wannan yunƙuri da bayyana shi a matsayin wata hanya ta mamaye harkokin mai, yana mai cewa idan aka ce matatar mai ɗaya ce za ta riƙa samar da mai ba za a samu gogayya ba wanda barazana ce ga samar da makamashi a mataki na dogon zango ga Najeriya.
Wannan ne ya jawo rashin jituwa tsakanin Aliko Dangote da Ahmed.
Daga baya Dangote ya zargi Ahmed da laifin cin hanci da rashawa da kuma cewa yana haɗa kai ne da ‘yan kasuwa na ƙasashen waje da na cikin gida wajen cuzgunawa matatun mai na cikin gida ta hanyar ci gaba da ba da lasisin shigo da man nfetur Najeriya.
Ya kuma zargi Ahmed da cewa yana rayuwa sama da samunsa, yana mai zarginsa da kai ‘ya’yansa 4 makarantu masu tsada domin karatun sakandare a ƙasar Switzerland wanda hakan ya jawo duba yuwuwar cin amanar ofishinsa da gaskiya wajen gudanar da ayyukansa.
Ahmed daga baya ya ajiye muƙaminsa biyo bayan wannan dambarwa.
Game da ƙarar da ya shigar a baya:
A shekarar 2024, matatar Dangote, ya shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/2024, inda ya nemi kotu da ta umarci NMDPRA da ta biya matatar diyyar Naira biliyan 100 kan ba da lasisin shigo da man fetur ga wasu ‘yan kasuwa da bari a shigo da man fetur.
‘Yan kasuwar da aka ambata a cikin ƙarar sun haɗa da NNPC Ltd, Matrix, AYM Shafa Limited, A.A. Rano Limited, T. Time Petroleum Limited da 2015 Petroleum Limited.
Ƙarar an shigar da ita ne a ranar 6 ga Satumbar 2024, lauyan wanda ake ƙara, Ogwu Onoja, ya buƙaci kotun da ta ayyana cewa NMDPRA ya saɓa sashen na 317(8) da (9) na dokar harkokin man feur (PIA) ta hanyar ba da lasisin shigo da man fetur.
Matatr Dangote ta ce za a ba da irin wannan lasisi ne kaɗai a lokacin da aka samu ƙarancin man fetur a ƙasa.
Sai dai a ɓangaren ‘yan kasuwar da ake ƙara sun mayar da martani a ranar 5 ga Nuwambar 2024 ta hannun lauyansu Ahmed Raji (SAN), inda suka buƙaci kotun ta yi watsi da iƙirarin da matatar Dangote ke yi, suna masu cewa akwai buƙatar bai wa kamfanoni damar yin gogayya wanda zai tallafa wa tattalin arziƙin Najeriya da tabbatar da masana’antar man fetur ta ci gaba da bunƙasa.
Sun ce sun cancanci samun lasisin shigo da man daga hukuamr NMDPRA a bisa tanadin dokar PIA, sashe na 317(9).
Sun kuma zargi matatar da ƙoƙarin mamaye kasuwar mai ta yadda zai zama shi kaɗai ne mai samarwa da raba wa da sanya farashin mai a Najeriya.
A watan Yulin 2025, matatar Dangote ta janye daga ci gaba da ƙarar da take na ƙalubalantar izinin shigo da man ba tare da faɗar dalilanta ba
