News
“Kamfanin Kera Motoci Na Ford Ya Sake Ɗaukar Injiniyoyin Da Ta Sallama Bayan AI Ta Gaza Maye Gurbin Ƙwarewarsu.”

Kamfanin kera motoci na Ford da ke Amurka ya sake ɗaukar wasu daga cikin ƙwararrun injiniyoyinsa da ya sallama aiki, bayan da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) ta kasa maye gurbin ƙwarewarsu kamar yadda kamfanin ya yi tsammani.
Ford ta fara amfani da fasahar AI ne domin rage kashe kuɗaɗe da kuma hanzarta gudanar da ayyuka a wasu sassan kamfanin, ciki har da sashen tabbatar da ingancin kayayyakin da ake kerawa.
Sai dai bayan wani lokaci da fara amfani da fasahar, kamfanin ya fahimci cewa AI ba ta iya gudanar da wasu muhimman ayyuka da gogaggun injiniyoyi ke yi, lamarin da ya haifar da koma baya a wasu fannoni.
Rahoton Bloomberg ya ce kamfanin ya sake ɗaukar sama da ma’aikata 300 masu kula da ingancin kayayyaki domin cike gibin da aka samu bayan dogaro da AI.
Mataimakin shugaban ɗaya daga cikin sassan injiniyoyin kamfanin, Charles Poon, ya ce AI na da amfani matuƙa, amma ingancinta ya dogara ne da irin bayanan da aka horar da ita da su.
Ya ce kamfanin ya fahimci cewa bai bai wa gogaggun injiniyoyinsa muhimmancin da ya dace ba, duk da irin ƙwarewa da gogewar da suka tara tsawon shekaru suna aiki.
A watan Oktoban bara ne Ford ta sanar da shirin faɗaɗa amfani da fasahar AI a sassa daban-daban na kamfanin, da nufin inganta aiki da rage kuɗaɗen gudanarwa.
Sai dai a ranar Larabar da ta gabata, Charles Poon ya bayyana cewa AI ba ta kai matsayin da za ta iya maye gurbin ƙwarewar injiniyoyin ɗan Adam ba.
Ya ce saboda haka ne kamfanin ya sake dawo da da dama daga cikin waɗanda suka bar aiki domin su ci gaba da tafiyar da ayyuka, tare da horas da sabbin ma’aikata.
A cewarsa, Ford ta fahimci cewa idan tana son ci gaba da bunƙasa amfani da AI, dole ne ta haɗa ƙarfin fasahar da gogewar ƙwararrun injiniyoyi, domin samun ingantaccen sakamako.
