News
Jami’an EFCC Sun Ƙwato Naira Biliyan 38.66 Da Manyan Kadarori A Badakalar Gyaran Matatun Mai

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da ƙwato tsabar kuɗi da suka kai Naira biliyan 38.66 tare da wasu manyan kadarori masu darajar miliyoyin nairori, a yayin da take ci gaba da bincike kan zargin badakalar kuɗaɗen gyaran matatun mai na gwamnatin tarayya.
Binciken hukumar ya samo asali ne daga zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran matatun mai, inda ake zargin an biya kuɗaɗe kan ayyukan da ba a kammala ba, yayin da wasu ayyukan kuma ake cewa ba a aiwatar da su kwata-kwata.
Peter Obi Ya Bukaci INEC Da Ta Wallafa Bayanan Shaidar Kammala Karatun ‘Yan Takara
Rahotanni daga hukumar sun nuna cewa binciken ya gano yadda ake zargin an karkatar da wasu kuɗaɗen zuwa asusun wasu kamfanonin bogi da kuma wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da tsofaffin jami’an gwamnati.
Shugaban EFCC ya bayyana cewa nasarar ƙwato kuɗaɗen da kadarorin wani muhimmin ci gaba ne a yaƙi da cin hanci da rashawa, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare dukiyar al’umma da kuma tabbatar da hukunta duk wanda bincike ya tabbatar yana da hannu a badakalar.
A wani mataki na binciken, hukumar ta ce ta rufe wasu asusun bankuna da ake zargin suna da alaƙa da lamarin, tare da ci gaba da tattara ƙarin hujjoji domin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
EFCC ta tabbatar da cewa binciken bai tsaya ba, tana mai cewa za ta ci gaba da bin diddigin duk wasu mutane ko kamfanoni da ake zargin sun amfana ko suka taka rawa wajen karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin farfaɗo da matatun man Najeriya.
