News
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi
Jami’an ‘yan sanda sun kama mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, mutumin da ake zargi da kafa wata hukuma ta bogi mai suna Presidential Fiscal and Infrastructure Projects Council (PFIPC), a garin Ogbomosho da ke Jihar Oyo.
Fitaccen lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, yana mai zargin jami’an tsaro da gudanar da abin da ya kira kama ba bisa ƙa’idar doka ba.
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
A cewar Falana, jami’an ‘yan sanda sun kai samame gidan iyalan Adeyemi, inda suka kama mahaifinsa tare da wani abokin iyali da ya je ziyara a gidan.
Ya ce babu wani tanadin doka da ya halatta kama mahaifin wanda ake nema saboda rashin samun damar kama ɗansa.
Falana ya ƙara da cewa Prince Adeyemi Adeniyi ya bayyana aniyarsa ta gurfana a gaban kotu domin kare kansa tare da gabatar da hujjojin da yake ganin za su tabbatar da matsayinsa.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda sun isa gidan da motoci huɗu kafin su tafi da mahaifin Adeyemi. Haka kuma, an ce mahaifiyarsa ta shiga cikin firgici bayan faruwar lamarin.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan hukumar PFIPC, wadda Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana a matsayin hukuma ta bogi da ba ta da sahalewar gwamnati.
Ana tuhumar Prince Adeyemi Adeniyi da laifuffuka da suka haɗa da ƙirƙirar takardu na bogi, bayyana kansa a matsayin jami’in gwamnati ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuffuka masu alaƙa. A halin yanzu, ana ci gaba da sauraron shari’arsa a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Falana ya jaddada cewa dole ne hukumomi su mutunta tsarin doka, yana mai cewa kotu ce kaɗai ke da ikon tantance ko mutum ya aikata laifi ko akasin haka.
