News
Mummunar Zaftarewar Kasa Ta Shafe Garin Wayanad A Kerala Ta Indiya
Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wata gagarumar zaftarewar ƙasa da ta afku a yankin Wayanad da ke Jihar Kerala ta ƙasar Indiya, bayan mamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki ana yi.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 7 ga Yuli, a kusa da gadar Meenakshi da ke Kalladi, inda ake gudanar da aikin gina hanyar rami da za ta haɗa gundumomin Malappuram da Wayanad.
An Sanya Ranar Ɗaurin Auren Lawan Garba da Maryam Sulaiman Sankara
Rahotanni sun ce ma’aikatan aikin ginin suna wurin lokacin da zaftarewar ƙasar ta afku, lamarin da ya janyo mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu shida da aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Hukumomi sun bayyana cewa ana fargabar har yanzu akwai fiye da mutum 10 da suka maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan ƙasa, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da aikin neman waɗanda abin ya shafa.
Jami’an Hukumar Kashe Gobara da Ceto tare da dakarun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NDRF) sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto, inda mazauna yankin ma suka shiga taimakawa wajen ceto mutanen da abin ya rutsa da su.
Ministan Kuɗaɗen Shiga na Jihar Kerala, AP Anil Kumar, ya tabbatar da cewa an tura jami’an NDRF 30 zuwa wurin domin ƙarfafa aikin ceto.
Mahukunta sun ce yankin ya samu ruwan sama mai nauyin milimita 265 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, abin da ake zargin shi ne ya haddasa zaftarewar ƙasar.
Bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna lokacin da zaftarewar ƙasar ta gangaro daga kan tsauni, tare da tura dimbin ɓaraguzan ƙasa zuwa ƙasa.
Rahotanni sun kuma nuna cewa mamakon ruwan sama da zaftarewar ƙasa sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 13 a ƙasashen Indiya da Bangladesh cikin kwanakin baya.
-
News3 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News3 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News3 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
