Connect with us

News

Na Ƙi Biyan Naira Miliyan 300 Kuɗin Fansa Lokacin da Aka Sace ‘Yan Uwana – Gwamna Dauda Lawal

Published

on

Dauda Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bayyana cewa ya ki amincewa ya biya kudin fansa har naira miliyan 300 da masu garkuwa da mutane su ka nema a lokacin da su ka sace yan uwansa a shekarar 2019.

Ya bayyana cewa ya zabi kin tattauna da masu laifin ne domin kada ya karfafa gwiwar fadada mummunar dabi’ar nan ta garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Mummunar Zaftarewar Kasa Ta Shafe Garin Wayanad A Kerala Ta Indiya

Gwamnan ya bayyana cewa shawarar tasa ta samo asali ne daga tabbacin da ya ke da shi na cewa biyan kudin fansa yana kara bai’wa kungiyoyin masu laifi kwarin gwiwar ci gaba da sace bayin Allah da ba su ji ba su gani ba.

Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis ya yin da yake jawabi a wurin taron kafar yada labarai ta ARISE News da THISDAY da aka gudanar a Abuja.

A wurin taron, ya kuma sabunta kiransa na kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin wani bangare na fadi-tashin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro a fadin kasar.

Advertisement

Acewar gwamnan masu garkuwar sun nemi naira miliyan 300 domin sakin ‘yan uwansa, amma ya ki amincewa ya tattauna da su ko ya biya ko kudin.

Gwamnan ya ce bayan kin biyan kudin, daga karshe masu garkuwar sun saki ‘yan uwan nasa bayan sun kwashe kusan watanni uku a tsare.

Lawal ya jaddada cewa abin da ya fuskanta ya kara tabbatar masa da imanin cewa biyan kudin fansa yana kara karfafa gwiwar kungiyoyin masu aikata laifuka ne kuma yana rura wutar ci gaba da garkuwa da mutane.

Gwamna Dauda ya bayyana cewa idan masu garkuwa da mutane su ka fuskanci cewa ba za su iya samun kudi daga wajen ‘yan uwan wadanda su ka sace ba ko gwamnati, za su karaya daga ci gaba da aika-aikar.

Gwamnan ya jaddada cewa matsayinsa bai canza ba tun a shekarun baya, yana mai cewa ba zai taba tattaunawa da masu laifi ba ko ya biyasu kudin fansa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending