News
Adamu Ladan Ya Gina Makaranta Don Tallafa Wa Ilimi A Dandume
Wani ɗan kishin al’umma, Hon. Adamu S. Ladan, FCAI, ya miƙa sabuwar makaranta mai ajujuwa shida ga Ƙaramar Hukumar Dandume da al’ummar Tudun Badole da ke Jihar Katsina.
An gina makarantar ne domin taimakawa wajen inganta damar samun ingantaccen ilimi ga yara da matasa a yankin.
Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 36 A Borno
An miƙa makarantar ga ƙaramar hukumar da al’ummar yankin ne a wani biki da aka gudanar a Tudun Badole ranar Juma’a.
Da yake jawabi a wajen bikin, Ladan ya bayyana aikin a matsayin gudummawarsa wajen tallafa wa ilimi da ci gaban al’umma.
Ya ce ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa, don haka ya buƙaci al’ummar Tudun Badole da maƙwabtansu su kula da makarantar tare da kare kayayyakin cikinta daga lalacewa da barna.
Ladan ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su ƙarfafa gwiwar yara, musamman ’yan mata, wajen neman ilimi da kuma amfani da damar da sabuwar makarantar ta samar.
Ya shawarci malamai da su mayar da hankali wajen bai wa ɗalibai ingantaccen ilimi da tarbiyya, yana mai cewa makomar Dandume, Katsina da Najeriya ta dogara da yadda ake koyar da tarbiyyantar da yara.
«“Ina kallon wannan aiki a matsayin ƙaramin gudummawa daga gare ni wajen tallafa wa ilimi da ci gaban al’ummarmu,” in ji shi.»
Ladan ya bayyana godiyarsa ga tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, bisa taimakon da ya bayar wajen ganin an samu damar aiwatar da aikin.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda; Shugaban Ƙaramar Hukumar Dandume, Alhaji Bashir Sabi’u Gyazama; da ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Dandume, Alhaji Yahaya Nuhu Mahuta, bisa goyon baya da haɗin kai.
Haka kuma, ya yaba wa shugabannin al’umma, ’yan kwangila da ma’aikatan da suka taka rawa wajen kammala aikin.
Ladan ya bayyana fatan cewa makarantar za ta taimaka wajen samar da ƙwararru da za su bayar da gudummawa wajen ci gaban Dandume da Jihar Katsina.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya sanya makarantar ta zama Sadaƙatul Jariya ga dukkan waɗanda suka bayar da gudummawa wajen samar da ita.
-
Uncategorized4 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News7 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
-
News3 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
