Connect with us

News

Dakarun Sojin Sama Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 36 A Borno

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ƙarƙashin Operation Hadin Kai, ta ce jiragen yaƙinta sun kashe kimanin ’yan ta’adda 36 a wasu hare-haren sama da aka kai a sassa daban-daban na Jihar Borno.

Hare-haren sun gudana ne tsakanin daren 21 ga Agusta zuwa safiyar 22 ga Agusta, 2026, bayan rundunar ta samu sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da binciken sama na leƙen asiri (ISR), wanda ya gano motsi da taruwar ’yan ta’adda a wasu yankuna.

Mutane Huɗu Sun Mutu Bayan Cin Amala A Kogi

A wata sanarwa da Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Joint Task Force North East, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Asabar, ya ce an kai hare-haren ne a yankin Aduwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno da kuma Buratai a Ƙaramar Hukumar Biu.

Ya ce wani jirgin leƙen asiri mai ɗauke da makamai ya gano wasu ’yan ta’adda a yankin Aduwa, inda bayan samun izinin kai hari, jirgin ya kai musu hare-hare biyu. Bayan tantance sakamakon harin, rundunar ta ce an tabbatar da kashe kimanin ’yan ta’adda 16.

Daga baya, jirgin ya sake gano wasu ’yan ta’adda kusan 10 da ke ƙoƙarin sake haɗuwa bayan sun watse daga wurin da aka kai harin farko. Rundunar ta ce an sake kai musu wani hari na musamman, inda aka samu nasarar tarwatsa su.

Advertisement

A wani hari na daban a Buratai, Ƙaramar Hukumar Biu, wani jirgin Operation Hadin Kai ya gano wasu ’yan ta’adda da suka taru a wani wuri. Bayan sa ido da samun izinin kai hari, jirgin ya kai musu farmaki, inda rundunar ta ce an kashe ƙarin ’yan ta’adda 10.

Rundunar ta ce hare-haren sun nuna yadda ingantaccen amfani da bayanan sirri da na’urorin leƙen asiri ke taimakawa wajen gano da kuma dakile motsin ’yan ta’adda kafin su zama babbar barazana ga sojoji da al’ummomin da ke fama da matsalar tsaro.

Ta ƙara da cewa ’yan ta’addan ba za su iya dogaro da watsewa, ɓoyewa ko fakewa a wurare masu nisa domin tserewa daga gano su ba.

A cewar rundunar, ci gaba da matsin lambar soji zai ƙara takura wa ’yan ta’addan damar gudanar da ayyukansu, tare da tarwatsa tsarin jagoranci da kula da ayyukansu da kuma raunana hanyoyin samar musu da kayan yaƙi.

Operation Hadin Kai ta ce hare-haren wani ɓangare ne na babban shirin rundunar na rage ƙarfin ’yan ta’adda da kuma samar da ingantaccen yanayin tsaro ga al’ummomin yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta bayyana cewa ana haɗa hare-haren soji da matakan da ba na yaƙi ba, ciki har da hulɗa da al’umma, yaɗa saƙonnin zaman lafiya, yaƙi da farfagandar ’yan ta’adda da kuma ayyukan jinƙai.

Advertisement

Ta ce yawan ’yan ta’addan da ke mika wuya a ’yan makonnin nan na nuna irin matsin lambar da ake yi wa ƙungiyoyin ta’addanci, tare da tabbatar da cewa akwai hanyar da za su iya barin tashin hankali su koma rayuwar zaman lafiya.

 

PRNIGERIA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending