News
’Yan Bindiga Sun Sace Mutune 60 Ana Tsaka Da Salla A Masallaci A Neja
’Yan bindiga sun kai hari wani masallaci a garin Dekara, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, inda suka yi awon gaba da mutane a tsaka da sallar Juma’a.
Rahotanni sun ce maharan sun isa garin da yawa, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su tattara wasu daga cikin masu sallar tare da tafiya da su zuwa cikin daji.
Ilimi Da Addini: Iqra’a Academy Nguru Ta Shirya Bikin Yaye Dalibai Da Masu Haddar Alƙur’ani
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma kai hare-hare wasu ƙauyuka biyu a Ƙaramar Hukumar Borgu a ranar Juma’a
Ya ce sama da mutum 60 maharan suka sace a Masallacin Juma’a na garin Dekara.
Sai dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da ainihin adadin waɗanda aka sace ba.
Mutumin ya ƙara da cewa babu wanda ya samu rauni a yayin harin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai binciki lamarin tare da yin ƙarin bayani.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta yi ƙarin bayani ba.
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News6 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
-
News2 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
