News
Allah Ya Yi Wa Kakakin Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, Rasuwa
Allah Ya yi wa kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, rasuwa.
Shugaban shiyyar hukumar na karamar hukumar Dambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru ne ya tabbatar da rasuwar ga Premier Radio 102.7 FM Kano.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Adaidaita Sahu A Kano
Marigayin, Saminu Yusuf Abdullahi, ya taka muhimmiyar rawa wajen isar da bayanai ga al’umma dangane da ayyukan hukumar da kuma abubuwan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Tuni aka yi jana’izar sa da misalin 8:30 na safiyar yau Laraba 7 ga watan October 2026 a jihar Kano
Muna roƙon Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahamarsa, Ya sanya Aljanna ce makomarsa.
Advertisements
