News
EFCC Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da Matashiya TV Wajen Yaƙi Da Laifukan Tattalin Arziki
Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC, ta ce za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da laifukan tattalin arziki da kuɗi.
Daraktan shiyyar EFCC ta Kano, Mataimakin Kwamandan Hukumar, ACE1 Friday S. Ebelo, ya bayyana hakan ne ranar Laraba 7 ga Oktoba, 2026, lokacin da Shugaban Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, ya kai masa ziyarar ban-girma a ofishinsa.
Wani Yaro Mai Shekara 9 Ya Ƙona Gidan Mahaifinsa Bayan An Zarge Shi Da Satar Kaza A Yobe
A cewar Ebelo, kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a da hana aikata laifuka, yana mai cewa ba za a iya cimma burin samar da Najeriya marar laifukan tattalin arziki da kuɗi ba tare da haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai ba.
Ya ce ayyukan EFCC sun haɗa da yaƙi da laifukan intanet, damfara, halatta kuɗaɗen haram, cin hanci a ɓangaren gwamnati da kuma ayyukan da ke cutar da tattalin arziki.
Ebelo ya ce yaɗa bayanai kan ayyukan hukumar na da muhimmanci wajen hana masu niyyar aikata laifi, da kuma wayar da kan jama’a, musamman matasa.
A nasa ɓangaren, Shugaban Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, ya ce kafar na son kafa dangantaka mai ɗorewa da EFCC.
Ya ce Matashiya TV ta mayar da hankali kan aikin jarida, ci gaban al’umma da ƙarfafa matasa, inda ya ce sun horas da matasa sama da 3,000 kan sana’o’i daban-daban.
Ya kuma ce kafar ta tsara shirye-shirye na musamman domin wayar da kan matasa da kuma nisantar da su daga aikata laifukan intanet da tashin hankali.
A ƙarshen ziyarar, ɓangarorin biyu sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙi da laifukan tattalin arziki da kuɗi a Kano da sauran sassan ƙasar.
