Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Shirin Rage Farashin Man Fetur Na Tsawon Kwanaki 30

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur amma a iya gidajen mai na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) na tsawon kwanaki 30.

Daily Trust ta rawaito cewa Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da tattalin aziƙin kasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Saƙon “Renewed Hope” Ya Isa Ga Jama’a — Waiya Ya Bukaci Mukarraban Shugaba Tinubu Daga Arewa Su Kai Saƙon Gwamnati Ga Jama’a

Oyedele ya ce za a samu rangwame kan farashin fetur a gidajen mai na NNPC na tsawon wata guda, inda za a bai wa masu motocin jigilar fasinjoji fifiko.

Ya ce: “Za a samu rangwame kan fetur a NNPC na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu harkar jigilar jama’a fifiko.”

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta cimma matsaya kan sabon farashin saukar da man fetur (landing cost), wanda za a rika duba shi duk wata.

Advertisement

Ya ce matakan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar man fetur, musamman masu zirga-zirgar jama’a da fasinjoji.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending