News
Babu Sunan Pantami Cikin Sunayen ‘Yan Takarar Gwamnan Gombe Da Inec Ta Fitar
Hukumar zaben Najeriya INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar zaɓen gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027, inda sunan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi batan dabo.
Rashin sunan Pantami a jerin ya zo ne bayan takaddamar da ta dabaibaye takararsa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ciki har da hukuncin babbar kotun tarayya da ta soke nasararsa a zaɓen fitar da gwani na farko tare da umartar jam’iyyar ta sake gudanar da zaɓen.
2027: Waiya Ya Buƙaci Ƙungiyoyi 50 Su Haɗa Kai Don Tallafa Wa Gwamna Abba Da Shugaba Tinubu
A ranar 29 ga Satumban, 2026, Pantami ya sake lashe zaɓen fitar da gwani na PDP da aka gudanar, inda ya samu ƙuri’u 2,054, yayin da Khamisu Mailantarki ya samu 389, Aliyu Usman Garry kuma ya samu 112.
