News
Allah Yayiwa Ismail Garba Gwammaja rasuwa, Tsohon Kakakin Ma’aikatar Lafıya Ta Kano
Allah ya yi wa Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Kula da Gidaje ta Jihar Kano, Ismail Garba Gwammaja, rasuwa bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin, wanda ya kasance gogaggen jami’in hulɗa da jama’a, ya yi aiki a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na Gwamnatin Jihar Kano, inda ya bayar da gudunmawa a fannin hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma har ya kai matsayin darakta.
Kotu ta soke tuhume-tuhume 8 kan zargin Adeniyi Adeyemi na samar da hukumar bogi
An gudanar da jana’izar marigayin a gidansa da ke unguwar Kuntau, da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, Ya kuma ba iyalansa, ’yan uwa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi.
Amin ya Rabbal Alamin.
