News
Kotu ta soke tuhume-tuhume 8 kan zargin Adeniyi Adeyemi na samar da hukumar bogi
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke tuhume-tuhume takwas da gwamnatin tarayya ta shigar kan Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da yin ikirarin zama Darakta-Janar na Hukumar Inganta Hulɗar Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa TA BOGI
Mai shari’a Mohammed Garba Umar ne ya yanke hukuncin soke tuhume-tuhumen a ranar Litinin, bayan gwamnatin tarayya ta shigar da bukatar dakatar da shari’ar.
Kotu Ta Tsige Ɗan Takarar APC Bayan Ta Gano An Sauya Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani
Gwamnatin ta bayyana cewa za a mayar da Adeyemi zuwa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, domin sake gurfanar da shi a gaban kotu.
A zaman kotun, Daraktan Masu Gabatar da Kara na Tarayya, Rotimi Oyedepo, babban lauya mai daraja ta SAN, ne ya gabatar da bukatar soke shari’ar.
Oyedepo ya shaida wa kotun cewa Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a ya sake nazarin takardun shari’ar Adeyemi da tuhume-tuhumen da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya fara shigarwa, inda aka gano wasu kura-kurai a cikinsu.
