News
Kotu Ta Tsige Ɗan Takarar APC Bayan Ta Gano An Sauya Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, Jihar Filato, ta tsige Mancha John Vincent a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC na kujerar Majalisar Dokokin Jihar Filato mai wakiltar Jos ta Kudu, tare da ayyana Ayuba Dalyop Mandung a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
A cewar jaridar Daily Trust, kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dorcas Agishi, ta yanke hukuncin ne bayan Mandung ya shigar da ƙara kan zargin sauya sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 20 ga Mayun 2026.
Kotun ta ce sauya sakamakon zaɓe bayan an sanar da wanda ya yi nasara ya saɓa wa doka. Ta kuma bayyana cewa ba a bai wa Mandung damar kare kansa yadda ya kamata ba.
Ta umarci APC ta miƙa sunan Mandung ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2027.
Haka kuma, kotun ta ci Vincent, APC da INEC tarar naira 500,000 kowannensu, tare da yin watsi da ƙorafe-ƙorafen farko da suka gabatar na neman a soke shari’ar.
