News
Gwamnatin Kano Ta Rufe Makarantu Masu Zaman Kansu Guda 9
Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu makarantu masu zaman kansu guda 9 saboda karya ƙa’idojin sabunta rajista da takardun shaidar gudanar da makarantu.
Shugaban Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano.
Kotu Ta Tsige Ɗan Takarar APC Bayan Ta Gano An Sauya Sakamakon Zaɓen Fidda Gwani
Ya ce rufe makarantun ya fara ne daga ranar 12 ga Oktoba, 2026, inda ya bayyana cewa hukumar ta gano makarantu 111 da ake zargin sun kauce wa hanyoyin da aka tanada na gudanar da rajista.
Makarantun da aka rufe sun haɗa da Zayyad Academy, Success International Schools, Sunshine International School, Perfect Schools, Al-Fa’iq International College, Mainasara International School, Shubla Academy, Darul Mu’uminat Comprehensive School da Hanan International School.
Baba Abubakar ya gargaɗi masu makarantun da kada su sake buɗe su ba tare da izinin hukumar ba, yana mai cewa duk makarantar da ta saɓa wa umarnin za ta fuskanci matakin shari’a.
