News
Kamfanin TikTok Ya Musanta Takaita Amfani Da Manhajar A Arewacin Najeriya
Kamfanin TikTok ya musanta cewa shi ne ya takaita amfani da manhajarsa a wasu sassan arewacin Najeriya, yayin da masu amfani da manhajar ke kokawa kan matsalar shiga da amfani da shafin.
Shugabar sashen sadarwa na kamfanin a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara, Keagile Makgoba, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Ta ce kamfanin na tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin da aka tabbatar.
“Za mu iya tabbatar da cewa TikTok ba shi ne ya sanya wannan takaita amfani da manhajar ba,” in ji ta.
Makgoba ta ce kamfanin na ci gaba da kokarin tabbatar da cewa al’ummomin da ke amfani da manhajar na iya samun damar yin hakan.
Advertisements
