Connect with us

Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Dakatar Da Sarkin Daura

Published

on

IMG 20261123 WA0067
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, daga gudanar da dukkan ayyukan hukuma har sai an kammala bincike kan zargin cin zarafin wata mata ‘yar ƙasar Australia da ake yi masa.

Haka kuma, gwamnatin ta kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike mai zurfi kan zargin da ake yi wa basaraken.

Adadin ‘Yan Najeriya Da Amurka Ke Shirin Kora Ya Kai 157

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu na jihar, Dr. Bala Salisu Zango, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2026.

A cewar sanarwar, Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin, wanda zai gudanar da bincike tare da miƙa rahoto da shawarwarinsa ga gwamnatin jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, baya ga dakatar da Sarkin daga ayyukan hukuma, an kuma hana shi gudanar da tafiye-tafiyen da suka shafi aikinsa na sarauta har sai an kammala binciken.

Advertisement

Gwamnatin Katsina ta tabbatar wa al’umma cewa za ta tabbatar da adalci wajen gudanar da binciken, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su mutunta doka da oda, sannan su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

 

 

NIGERIAN TRACKER 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending