Connect with us

Labarai

Ba Zan Taba Yin Sulhu Da Yan Ta’adda Ba —Gwamnan Jihar Zamfara

Published

on

Dauda Lawal
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na rashin tattaunawa da ‘yan bindiga da ke ta’addanci a jihar.

Gwamnan ya faɗi haka ne a yau Alhamis a wajen bikin yaye masu gadin gandun daji na Zamfara da aka gudanar a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Gada Biyu a Gusau.

An Hallaka Wani Mutum Har Lahira Kan Gyaran Takalmi A Kano

Sama da masu gadin daji 1,000 a Zamfara sun samu horaswa a kan amfani da makamai, motsa jiki, shirye-shiryen yaƙi, alaƙar farar hula da sojoji, haɗin gwiwar tsaro, hulɗa da al’umma, da kuma bin doka.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ƙaddamar da shirin masu gadin daji masu ɗauke da makamai a ranar 24 ga Mayu, 2025, domin horar da mazauna yankunan karkara su kare dazuzzuka da sauran yankunan da ba a kula da su ba a faɗin ƙasa.

A wajen taron, Gwamna Lawal ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro bisa goyon bayan gwamnatin tarayya ga shirin masu gadin daji.

Advertisement

Ya yaba wa hukumomin tsaro, mai gudanar da horaswar, da malamai bisa shirya waɗanda suka kammala horaswa domin hidima.

“Ga iyalansu waɗanda suka kammala horaswa, na gode muku da goyon baya da ƙarfafawa da kuka ba su,” in ji gwamnan.

Gwamna Lawal ya ce akwai buƙatar gaggawa ta ƙwato manyan dazukan yankunan Zamfara da ba a kula da su ba, waɗanda suka zama mafaka ga ‘yan bindiga, masu laifi da ‘yan ta’adda.

“Dole ne mu gaggauta ƙwato manyan yankunan Zamfara da ba a kula da su ba, waɗanda suka zama mafaka ga ‘yan bindiga, masu laifi da ‘yan ta’adda.

“Wannan zai buƙaci ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tarayya da na jiha, da kasancewar tsaro mai ɗorewa, da kuma dawo da ayyukan jama’a.

“Manufarmu ita ce tabbatar da cewa iyalai da suka rasa matsugunansu za su iya komawa gida lafiya, kuma al’ummomi za su iya noma, kasuwanci da sake gina rayuwarsu,” in ji shi.

Advertisement

Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ta kashe makudan kuɗaɗe a kan hukumomin tsaron jiha cikin shekaru uku da suka gabata, inda ta samar da kayan aiki, sufuri, sa ido da tallafin dabaru yaki da ‘yan ta’adda.

“Mun samar da sama da motocin yaƙi masu sulke (Armoured Personnel Carriers) guda 30, da motoci masu ɗaukar kaya guda 200 don aiki, da motoci Toyota Buffalo guda 20, da babura na musamman sama da 1,000, da ƙarin motoci da babura ga masu gadin al’umma na gida (Homegrown Community Protection Guards).

“Mun kuma samar da jiragen sa ido marasa matuƙi (drones), ciki har da wanda ke iya tashi har mita 80, ya kai nisan kilomita 50 kuma ya ci gaba da aiki na tsawon awanni takwas ba tsayawa, wanda ke inganta leƙen asiri, sanin halin da ake ciki da daidaita aiki a wurare masu wahala,” in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending