Connect with us

News

Zan Yi Kokari Wajen Sauke Nauyin da aka Ɗora min a matsayin Mai Baiwa Gwamna Shawara Kan Yada Farfaganda – Naburaska

Published

on

Spread the love

Daga Muhammad Muhammed zahraddini

 

 

Advertisement

Mataimaki na musamman Ga Gwamnan Kano mustapha Badamasi Naburaska Ya Bayyana Cewa zai aiki tukuru wajen sauke nauyin da aka Dora masa a matsayin Mai Baiwa Gwamna Shawara a Fannin yada farfaganda.

Mustapha Badamasi Naburaska Ya Bayyana Hakan yayin zantawarsa da gidan Rediyon Guarantee a Kano.

Ya ce daga cikin ayyukan da a ka dora masa sun Hada da bayyana dukkan wasu ayyuka da suka shafi gwamnati ga al’umma da kuma Kawo hanyoyin bunkasa masana’antar Kannywood wadda za tayi Gogayya da sauran takwarorinta dake sassan kasarnan.

Advertisement

 

ya Kuma Yi Karin Haske Game da cece kuce da akeyi Game da mukaminsa na Mai Baiwa Gwamna Shawara akan Farfaganda Harma yayiwa wakilinmu Karin Haske Game da wannan Kalma da ake Tafka mahawara akanta.

 

Advertisement

A karshe Musstapha Badamasi Naburaska ya ce Fatan sa shi ne ya sauke nauyin da aka dora masa dn Ganin Kwalliya Tabiya Kudin Sabulu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *