Connect with us

News

Kotu a Jihar Kano ta ba da belin injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Wata kotu a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya.

Kotun mai lamba 58 da ke zamanta a unguwar Nomansland ta bayar da belin ne kan naira miliyan daya, tare da gindaya masa wasu sharuda da sai ya cika belin zai bayu.

Mai shari’a Aminu Gabari ya ce bayan biyan kudin da Dan Sarauniya zai yi sai ya kuma ajiye fasfo dinsa na tafiya.

Advertisement

Kazalika zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa, dole na farko ya zama mai garin kauyen Sarauniya wato kauyen da ya fito, na biyun kuma dole ya zama limamin garinsu ko kuma kwamandan Hizban garin.

A ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama Injiniya Mu’azu a Abuja babban birnin Najeriya.

An kuma mayar da shi jihar Kano inda ‘yan sanda suka gabatar masa da tuhume-tuhumen da ake zarginsa da su, na keta mutunci gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *