Hukumar kashe gobara ta Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce mutum shida ne suka mutu a gobara 114 da aka yi a jihar a yankuna uku kacal.
Jaridar TheNation ta ruwaito cewa daraktan hukumar Mista Paul Aboi, Director, ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Ya ce an samu gobarar ne a yankunan Kaduna da Zaria da kuma Kafanchan.
Aboi ya ce hukumarsu ta ceto mutane huduwadanda ba su jikkata ba, yayin da mutum 8 suka jikkata sakamakon gobarar.
“Hukumar ta ceto dukiyar da ta kai darajar biliyan 4,3, yayin da dukiyar da aka yi asara ta kai darajar miliyan 785 a cikin wata guda, in ji shi.