Connect with us

News

Na nemi Buhari ya shiga tsakanina da EFCC – Rochas Okorocha

Published

on

Spread the love

Daga Muhammed Muhammed zahraddini

Tsohon gwamnan Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya kuma sanata a yanzu, Rochas Okorocha, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya shiga tsakaninsa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC.

Okorocha ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Buhari a fadar shugaban kasar, inda ya ce ya gabatar wa da shugaban wannan bukata kan hukumar ta daina yawan muzanta shi da neman harzuka shi a kan shari’ar zargin almundahana ta naira biliyan 2.9, abin da kusan take yi masa a kullum, a cewarsa.

Sanatan ya ce ya nemi Shugaba Buhari a matsayinsa na mai mutunta doka da son kiyaye da ka’ida da ya sa baki kan al’amarinsa da hukumar ta EFCC don ta bi umarnin kotu.

Advertisement

“Ina da hukunci da umarnin kotu biyu, hukunci daban-daban har uku a wurare daban-daban wadanda suka hana EFCC cin zarafi da harzuka ni, amma EFCC ta kekasa kasa ta ki bin doka, saboda haka dole ne na gaya wa shugaban kasa cewa a sa EFCC ta bi dokar da ta kafa ta, wanda kuma idan da ba doka to da ba EFCC,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “kuma ta daina azarbabi kan bin duk abin da ya shafe ni”.

Okorocha ya ci gaba da cewa: “Kuma na tuna wa Shugaban Kasa cewa (idan ba a manta ba) a wani lokaci, EFCC ta yi ikirarin cewa ta kwato jumullar naira bliyan 5.9 daga asusun bankina, abin da kotu ta gano cewa ba gaskiya ba ne, ko kuma a ce ma suna nuna son-kai da azarbabi da riga-mallam-masallaci a kaina.

Advertisement

“A kan haka kotu ta zartar da cewa kada su kara bincikena da cin mutuncina. Wannan ma ba ta bi ba. Kotu ta kuma umarci EFCC ta saki fasfona, EFCC ta ki bin umarnin.

”Kotu ta umarci EFCC ta biya ni naira miliyan 500 na ɓatanci, EFCC ba ta biya ba. Maimakon ma ta biya sai ta bari a ranar da zan kaddamar da takarata ta neman shugaban kasa sai ta faɗa wa ‘yan jarida cewa an gurfanar da ni a kotu a kan aikata wasu laifuka na almundahanar naira biliyan 2.9, ba kuma bliyan 5.9 ba.

“Saboda haka na ce a matsayinsa na shugaban Najeriya, kuma wanda ke tsaye a bangaren kiyaye doka ya ja hankalin EFCC a kan wannan.”

Advertisement

Okorocha wanda ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasar a zaben 2023, ya ce ya tattauna wasu batutuwan da Shugaba Buhari a yayin ganawar tasu, inda ya bayyana bukatar karfafa jam’iyyarsu ta APC daga tushe.

Ya ce, shugaban ya yi alkawari musamman ma cewa lokacin da ‘yan siyasa za su rika samun mulki daga Abuja, ba tare da goyon baya daga talakawa daga tushe ba ya wuce, ba za a kara yarda da hakan ba a jam’iyyarsu ta APC

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *