Connect with us

News

ASUU ta yanke kauna da gwamnatin Buhari

Published

on

FB IMG 16439797733547090
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

Kungiyar malama jami’a ta Najeriya ASUU ta nuna shakkunta game da cika alkawuran da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka na samar da mafita ga matsalolin da fannin ilimin kasar ke ciki, musammam jami’u.

Kungiyar ta ce za ta fara yajin aikin sai baba ta gani nan ba da jimawa ba.

Kungiyar ta bayyana lamarin da ke faruwa a halin yazu da “abin kunya” yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da kare tsarin biyan kudi na IPPIS duk da zargin cewa akwai almundahana a cikinsa, kamar yadda ya bayyana a cikin rahoton da babban akantan tarayyar Najeriya ya gabatar a gaban Majalisar dattawan kasar.

Advertisement

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ASUU ta nuna fushinta kan yadda aka rika zaman sasanci tsakaninta da gwamnati kan yadda za a farfado da ilimi sai dai gwamnati ta gaza dabbaka abin da take ta ikirari a baya.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *