Connect with us

News

Kotu ta sassautawa Muaz Magaji sharuɗɗan beli

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Kotun Majistare mai lamba 58 da ke zaman ta a unguwar Nomansland ta sassautawa Muaz Magaji, babban ɗan adawar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sharuɗɗan beli, bayan da ya gaza cika wadanda a ka gindaya masa a farko.

Kotun Majistare ɗin, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aminu Gabari ce ta bada belin Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan-Sarauniya, bayan ta aike da shi gidan yari tun a ranar 31 ga watan Janairu.

Kotun dai na tuhumar Magaji da laifuka huɗu da su ka haɗa da ɓata suna, cin mutunci da gangan, ƙarya da nufin zubar da kima da kuma ta da hankali, laifukan da su ka saɓa da sashe na 392, 399 da 114 na kundin dokar Kano ta 1999, amma kuma ya musanta duka laifukan.

Advertisement

Ƙa’idojin belin da kotun ta bayar da farko sun haɗa da naira miliyan 1 da kuma waɗanda za su tsaya masa mutum biyu.

A cikin mutum biyun da za su tsaya masa, in ji alƙalin, a kwai Dagacin ƙauyen Ɗan-Sarauniya, sai kuma Kwamnadan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ko kuma Babban Limamin Ƙaramar Hukumar.

Hakazalika kotun ta bukaci Magaji da ya kai mata fasfo ɗin shi na tafiye-tafiye, inda su ma mutum biyun da za su tsaya masa sai sun kai hotunan su.

Advertisement

Sannan kotun za ta tura ma’aikatan ta su duba gidajen mutum biyun da za su tsayawa Magaji.

Sai dai kuma Magaji bai iya cika waɗannan ƙa’idoji ba sakamakon babban limamin Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa bai je ya wakilci shi ba.

Ganin haka ne sai sai lauyan Magaji, Ghazzali Ahmad, ya miƙawa alƙalin kotun roƙon su na a sassauta sharuɗɗan belin.t

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa a zaman kotun na jiya Juma’a, alƙali Gabari ya karɓi rokon sassauta belin, inda ya umarci a kawo babban limamin ƙauyen su Magaji ɗin, wato ƙauyen Ɗan-Sarauniya, a maimakon na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa.

Kotun ta kuma umarci Magaji da ya biya gilashin motar Gidan Yari da a ka faɗa lokacin da a dauko shi za a kawo shi kotun.

Yanzu dai za a zuba ido a gani ko limamin Ɗan-Sarauniya ɗin shima zai zo, ko kuma Magaji zai ci gaba da zama a gidan kaso, yayin da ya doshi kusan makonni biyu a can.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *