News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Tan 1,500 Na Irin Alkama
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya za ta rabawa manoma Irin alkama mai jure zafin rana da yawansa ya kai tan dubu 1 da 500 a bana, ƙarƙashin shirin tallafawa aikin noma kashi na 1.
Shugaban shirin a matakin ƙasa, Ibrahim Mohamed Arabi ne ya bayyana haka, a ziyarar da ya kai wani kamfanin takin zamani a ƙaramar hukumar Madobin jihar Kano.
Zanga Zangar Tsadar Rayuwa: An Kashe Aƙalla Mutum 24, An Kama 1,200 — Amnesty International
Arabi ya ce sabon Irin zai taimaka wajen magance ƙarancin alkama da tsadarta, yayin da a gefe guda zai tallafawa ƙananan manoma. Ya ƙara da cewa kamfanin Al-Yuma da ke samar da Iri, taki, da sauran kayayyakin noma na Jihar Kanon ne zai samar da Irin alkamar.
A zantawarsa da RFI Hausa, shugaban ƙungiyar manoman Najeriya AFAN, Dr Farouk Rabi’u Mudi, ya ce matakin zai yi tasiri matuƙa wajen kawo cigaban fannin noma musamman na alkama.
Dr Farouk ya kuma ce cigaban zai inganta yanayin yadda ake samar da alkama, kasancewar ita bata fitowa a lokacin zafi, sai dai samar da wannan Iri mai jure zafi zai sanya a samu wadatarta.
