News
Gobara Ta Kone Wasu Shaguna a Kasuwar Kofar Wambai Dake Birnin Kanon Dabo

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rahotanni sun bayyana cewa wata gobara da ta tashi da safiyar yau Lahadi ta kone wasu shaguna a kasuwar Kofar Wambai dake birnin Kano.
Wutar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asubahin yau, a Layin ‘yan Kabeji, kusa da shagunan masu siyar da kayan gwanjo. Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta fara ne daga wani shago kafin ta fara bazuwa zuwa wasu shaguna dake makwabtaka.
Yan-sanda Sun Kama Magidanci Da Ya Kashe Matarsa Kan Abincin Buda Baki A Bauchi
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta isa wurin domin dakile wutar, yayin da har yanzu ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, haka kuma ba a bayyana adadin asarar da aka tafka ba.
Wasu ‘yan kasuwa sun bayyana damuwarsu kan yadda gobara ke ci gaba da afkuwa a kasuwannin jihar, suna mai kira ga hukumomi da su kara daukar matakan kariya.