Sports
Dembele Ne Gwarzon Ballon d’Or Na 2025
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Dan wasan ƙasar Faransa da PSG, Ousmane Dembele ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekara ta 2025.
An bayyana ɗan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar a yau Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a ɗakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a ƙasar Faransa.
Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa ɗan wasan da ya burge a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da ɗanwasan ya bayar ga ƙungiya da kuma ƙasarsa.
Tun farko an fitar da jerin ƴanwasa 30 cikin waɗanda ake sa ran za su lashe kyautar Ƙwazon da Dembele ya nuna
Dembele ya buga wasa 53 a kakar bara, inda a ciki ya taka leda na minti 3,483.
Ɗan’wasan na Faransa ya zura ƙwallo 35, sannan ya taimaka aka ci ƙwallo 14 a kakar baki ɗaya. Haka zalika ya taka rawar gani wajen taimakon ƙungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi.
Ya zura ƙwallo 21 a wasa 29 da ya buga a gasar Ligue 1, inda ya ƙarƙare gasar a matayin wanda ya fi zura ƙwallo, sannan ya lashe kyautar gwarzon ɗan’wasan gasar.
Haka kuma shi ne gwarzon ɗan’wasan gasar Champions League, inda ya zura ƙwallo takwas, sannan ya taimaka aka ci shida.
Ɗan asalin ƙasar Faransa, Dembele ya nuna bajinta a gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi, inda ya zura ƙwallo a ragar Bayern Munich da Real Madrid a wasannin zagaye na biyu.
Lanine Yamal na kungiyar Barcelona shine ya zo na biyu a kyautar, bayan da ya lashe gwarzon matashin ɗanwasan na shekerar 2025.
Yamal ya buga wasa 55, inda a ciki ya yi wasa na minti 4,548, sannan ya zura ƙwallo 18, ya kuma taimaka aka ci ƙwallo 21.
Ɗan’wasan mai shekara 18 yana cikin zaratan waɗanda suka taimaka wa ƙungiyar Barcelona ta lashe kofuna guda uku – La Liga da Copa del Rey da Supercopa de Espana.
Ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasan La liga a watan Satumba, sannan yana cikin gwarazan ƴan’wasan gasar La liga da Champions League.
