Sports
Manchester United Da Arsenal Za Su Fafata A Old Trafford
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Wasan hamayyan zai kasance wasan farko ga dukkannin kungiyoyin guda biyu yayin da za’a fafata wasan a babban filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Manchester united wato old traffird da misalin karfe 4:30 na yammaci.
Gasar ta dawo ne ranar Juma’a bayan hutun kwanaki 82, inda Liverpool ta doke Bournemouth da ci 4-2. A jiya kuma Manchester City ta lallasa Wolves da ci 4-0, yayin da Tottenham Hotspur ta doke sabon shiga gasar, Burnley, da ci 3-0 a wasan farko na Thomas Frank.
Allah Ya Yi Wa Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami Rasuwa Yana Da Shekaru 81 A Duniya
Sai dai duk da wadannan sakamako, ziyarar Arsenal zuwa Old Trafford ce ta fi daukar hankalin jama’a duba da yadda dukkannin kungiyoyin suka cefano zaratan Yan kwallo masu zira kwallo a raga
Manchester United ta kammala kakar bara cikin mawuyacin hali, inda ta kare a matsayi na 15 a teburin gasar kuma ta sha kashi a wasan karshe na Europa League hannun Tottenham.
Sabon koci, Ruben Amorim, ya dauko sababbin ‘yan wasa uku — Matheus Cunha, Bryan Mbeumo da Benjamin Sesko — domin inganta karfin ‘yan gaba. Duk da haka, babban dan wasan da yake nema, Viktor Gyokeres, ya koma Arsenal.
A bangaren Arsenal kuwa, Gyokeres na daga cikin sababbin ‘yan wasa shida da suka iso kungiyar, ciki har da Christhian Mosquera, Kepa Arrizabalaga, Martin Zubimendi, Noni Madueke da Christian Norgaard.
kociyan Arsenal Mikel Arteta yace wannan kakar za ta kasance mai matukar muhimmanci. Bayan karewa a matsayi na biyu na tsawon kakanni uku a jere, akwai bukatar ya dauki kofin Premier League domin tabbatar da nasarar shirinsa.
Arsenal ta fara kakar da nasara a wasan farko, kuma akwai matsin lamba a kan tawagar Arteta ta fara kakar da karfi kamar yadda suke fata ta kare da daukar kofin.
