Connect with us

Politics

Daga MAKAFI Zuwa AWAKAI: Baje-kolin Siyasar Tumasanci Da Bautar Gumakan Siyasa.

Published

on

IMG 20250905 WA0009
Ibrahim Ishaq (Ɗan’uwa Rano)
Spread the love

DAGA IBRAHIM ISHAQ ƊAN’UWA RANO

A lokacin da mutane suka rungumi mummunar siffa kamar ‘MAKAFI’ ko AWAKAI’, ba demokraɗiyya su ke yi ba, suna sarayar da mutunchinsu ne. Kuma demokraɗiyya ba za ta taɓa wanzuwa ba tare da cikakken ƴancin kai ba.

Da farko dai zan fara yin godiya ga malamina Dr. Auwalu Anwar, wanda cikin maƙalarsa mai taken SAWABA zuwa ASARA, na samu ƙarin ilimi da cikakkiyar fahimtar wanene Kwankwaso da Kwankwasiyya, wanda shi ne ma ya buɗe min idanu tare da ƙarfafa min gwiwa, wajen rubuta tawa gajeriyar fahimtar, amma a ɓangaren yadda siyasar tumasanci ke samun gindin-zama a tsakanin al’ummarmu, kama daga kan masu mulki zuwa mabiya.

Bayan Samun Ruwan Sama Mai Ƙarfi, Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Sabon Gargadi Ga Jama’a

Idan aka ce siyasar tumasanci ba ta tsaya iya kan kalaman mabiya da ke rusa darajarsu ta Ɗan’Adamtaka ba, har ma da yasashshen zance da ke fita daga bakin su jagorori zuwa ga mabiyansu, wanda a wasu lokutan bayan raini ga janibin Ɗan’Adam da Allah Ya karrama, suke kuma rusa tarbiyya da haddasa tsageranci da isgili a tsakanin matasa.

Advertisement

Kalma daga Mahaliccinmu tana iya zama mabudi game da daraja da Ɗan’Adam ke da ita, wanda Allah da Kansa Ya ke fadin cewa Ya karrama Ɗan’Adam. A ta’aliƙin malamai, ma’ana Ɗan’Adam ba abin wulakantarwa ba ne. Idan kuwa mun yarda da haka, me ya kawo mu kira kanmu da MAKAFI bayan Allah bai jarabcemu da ciwon makanta ba? Ina dalili na mu kira kanmu AWAKAI? A’ah, wani salo ne na jaddada biyayyarmu ga wanda yake shugaba a cikin tsarin da muka yi imani da shi, ba tare da la’akari da gane cewa hakan yana da hadari ga rayuwarmu ba.

Koda yake magana ta gaskiya idan za a yi adalchi tare da waiwaye game da tarihi, za a ga cewa ba Kwankwaso ko mabiyansa ne farau ba a kan wannan mugunyar dabi’ah ta tumasanci, hasali ma ta samo asali da wanzuwa cikin al’ummarmu ne tun daga jamhuriya ta biyu, zamanin mulkin tsohon gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar Kano marigayi Abubakar Rimi, wanda ana iya cewa wani salon da Kwankwaso ke amfani da shi a siyasance, ya koya ne daga Marigayi Limamin Canji.

A zamanin da Marigayi Rimi ke kan ganiyar farin jini, an tabbatar da cewa ya samu nasa makafin mabiyan, domin a cikinsu an samu masu taɓargazar cewa ko wuta Rimi ya fada za su bishi. Ko da yake hakan ba lallai ya zo da mamaki ba, idan aka yi la’akari da cewa Rimi ya yi farin jinin da har yanzu Kwankwaso bai yi irinsa ba. Akwai malamai da masana tarihi da dama da suka tabbatar da hakan, cikinsu har da shugaban Majalisar Malamai ta jihar Kano kuma tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADC Ibrahim Khalil, yayin wata tattaunawa da na yi da shi a cikin shirin Bakon Mako, ya gaskata wannan magana. Haka nan shima tsohon sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar NNPP a Kano kafin ta dare gida biyu Musa Nuhu Yankaba, ya tabbatar da wannan magana bayan sun raba layi da kwankwasiyya. A yanzu haka shi ne sakataren jam’iyyar ta NNPP na Kano a tsagin kayan marmari.

Ɗabi’ar tumasanci akwaita cikin harkokin siyasa tun kafin zamanin Rimi – A wata ruwayar ma an ce hatta fitattun yan siyasa a zamanin su Mallam Aminu Kano da ake Tabo da Santsi, akwai jagororin da suke da irin wannan rashin linzamin a harshe, kuma sun samu biyayya daga masu take musu baya.

Advertisement

Idan ka zo nan kusa-kusa a zamani irin namu, mun gani kuma mun ji jagororin da suke yin kalamai marasa tsafta, cike da raini ga janibin Ɗan’Adam. Misali: A kwanakin nan shugaban jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya yi shuhra wajen furta lafazin ‘ko da tsiya ko da tsiya-tsiya’, baya ga kalmomi munana masu kamanceceniya da zagi ga abokan hamayyarsu. Bayan shi mun ga lokacin da Alhassan Ado Doguwa, wato wakilin Doguwa da Tudunwada a Majalisar Tarayya, shima ya tara mabiya yana tambayarsu ‘shin 2023 wa za ku zaɓa’? Su kuwa mabiyan sai amsawa suke yi da APC. Amma duk da haka da taro ya zuga shi, bai rufe baki ba sai da ya ɗura musu ashariya. Tabbas, zagi ne ya biyo baya, cewar ‘Kai wai idan ba ku zaɓi APC ba Ubanku za ku zaɓa’?

Abin mamaki a wannan lokaci babu wani daga cikin masu tafiya tare da shi ko magoya bayansa, da ya taka masa birki, ko haska masa cewa wannan lafazi fa kuskure ne, sai ma ihun farin ciki da suke yi. Wannan ya haska yadda siyasar tumasanci ke samun gindin zama a tsakanin jagorori da mabiya.

Ko da a maƙwabtan jihohi akwai misalai irin wannan, wanda gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi Ɗanmoɗi har ƙokarin mayar da shi ma’asumi wasu mabiya ke yi, ta hanyar ɗorashi a kan tafarkin cewa baya kuskure, komai ya yi daidai ne. A cikin salon da suke yi masa kirari da shi wai Mallam yana kan daidai.

Ni kuma a iya fahimtata da gwamnan Jigawa a matsayinsa na malami, ya san cewa wannan kalma da suke jingina masa kuskure ne, hasali ma ya sani babu wani wanda ya isa ya ce komai ya yi daidai ne, sai Allah SWT, da kuma masoyinmu Annabin Rahama SAW da aka tsaftace shi daga kowanne irin kuskure.

Advertisement

To idan gwamna ya yarda haka ne, me yasa ya ke bari magoya baya suke gaya masa, kuma alamun jin dadi ke bayyana a fuskarsa idan an faɗa? A nan ma’anar tumasancin ta bayyana, su mabiya sun san ƙarya suke gaya masa, shima ya san ƙaryar ake gaya masa cewa yana kan daidai, amma kuma duk da haka sun amince da wannan lamari saboda siyasa.

To amma inda gizo ke saƙar ko kuma in ce inda ta fi zafi shi ne ɓangaren Kwankwasiyya, a Kano, wadda mabiya da dama a wannan tsari suka amince da kiran kansu da dabbobi bayan makauniyar biyayya, don kurum su farantawa Oga. Zazzare idanu da Kwankwaso ke yi a lokacin da ya tara MAKAFINSA da AWAKANSA, tare da irin laffuzan da yake amfani da su wajen isar da saƙonsa na siyasa, ya sanya a kullum tsagerun cikinsu suke jin basu da Gunkin-bauta a siyasance sai Kwankwaso, kuma sun yarda ko me ya yi daidai ne.

Cikin kundin adana bayanaina na ci karo da wani faifan bidiyo da Kwankwaso ya tara jama’a yana bayyana musu irin ɗawainiyar da ya yiwa ƴaƴan talakawa a fannin ilimi, ƴaƴan waɗanda ba kowa ba ya mayar da su sun zama mutane. A dalilin wannan hidima da ya yi, yake ƙalubalantar duk wanda ya fito daga ahalinsu mai tuƙa abin hawa (A daidaita sahu) cewar “idan har baka saka hoton Kwankwaso a bayan Babur ɗinka ba ma sai Allah Ya tsine maka”

Wani abu da ya faru a kwanakin nan, ya ƙara tabbatar min da abin da malamina Dr. Auwalu Anwar ya faɗa, cewar ‘Kwankwaso ɗan damfarar siyasa ne, mai amfani da ƙidahumancin mabiyansa don ya ci da guminsu’. Lokacin wani taro da ya haɗa na masu biyayyar tumasanci ga tsarinsa, ya gayawa duniya cewar “Muna da Jam’iyya kuma muna jin daɗin zama a cikinta,…. duk wanda yake son magana da mu ƙofarmu a buɗe ta ke ga ƙawance”.

Advertisement

A zahirin gaskiya wannan lafazi bai yi kama da na wanda yake da kishin ƙasa da samar da shugabancin ƙwarai ba, domin a lokacin da mutane irin su Atiku Abubakar da ya samu ƙuri’ah kusan miliyan 7 a zaɓen da ya gabata, da Peter Obi da ya samu ƙuri’ah miliyan 6 da motsi, a ce sun sadaukar da duk wani jin kansu sun haɗu a ƙarƙashin tafiya guda domin ceto Najeriya, amma Kwankwaso da yake da ƙuri’ah miliyan 1, wai ya ja tunga ya ce shi yana nan a matsayin jagora mai runduna, sai dai in an damu da neman gudunmawarsa a zo a yi magana da shi, iya wannan lissafin kaɗai zai baka hasken cewa tabbas, Kwankwaso ɗan kasuwar siyasa ne mai mutakabbiranci irin wanda Allah baya so, kuma ba ƙasar ce a gabansa ba.

A taƙaice dai, duk abin da magoya bayansa ke yi na rashin ɗa’a ga mutane masu daraja, ko tumasancin yin makauniyar biyayya a gareshi har ma da danganta kansu da dabbobi, bai taɓa tsawatarwa ya ce su bari ba, wasu lokutan ma sai dai ka ga alamun jin daɗi a fuskarsa saboda ya samu yadda yake so. Babbar illar da wannan salon siyasa zai iya haifarwa a nan gaba, mai muni ne har ga shi Kwankwaso, kuma tarihi ba shi da rangwame ga kowa.

Makanta ta zuciya tafi makanta ta ido muni. Wanda ya yarda ya ɗauki kansa a matsayin MAKAHO ko kuma ya danganta kansa da AWAKAI, haƙiƙanin gaskiya ya amince da zama mai matacciyar zuciya, kuma ba shi da iko a kan tunaninsa. Domin AWAKAI ba sa yin tambaya, ba sa yin gwagwarmaya, haka nan kuma ba sa yin tunani – kawai bin umarni suke yi.

Idan Ɗan’Adam ya rage darajar kansa zuwa ga wannan mataki a matsayin biyayya, to siyasa ba ta amsa sunanta siyasa ba, ta zama bautar gumakan siyasa.

Advertisement

Wannan mugunyar ɗabi’ar biyayya a makance babbar barazana ce ga demokraɗiyya. Tana kange ƴan siyasa daga amsa tambayoyi ko ladabtarwa, tana kuma hana muryoyin hamayya yin tasiri, wanda hakan ke samar da yanayi da rashin iya aiki da cin hanci ke bunƙasa ba tare da shamaki ba. Gwargwadon yadda mutane ke alfahari da kiran kansu MAKAFI ko AWAKAI, gwargwadon yadda suke cigaba da shigar da kawunansu cikin sarƙar bauta.

Abu mafi muni fiye da haka shi ne yadda wasu ke jin daɗin rungumar wannan tumasanci. Kiran kanku “AWAKAI” domin ku yi wa wani ɗan siyasa biyayya ko hidima ba tawali’u ko ƙanƙan da kai ba ne – tumasanci ne. Wata alama ce ta bayyane cewa hankalinku da tunaninku kun sadaukar da shi kacokan zuwa ga siyasar tumasanci da son zuciya. Al’ummar da ta ke murna da irin wannan tozarci ba za ta iya gina makoma a kan adalci, gaskiya da nagarta ba.

Ina fata wannan taƙaitaccen tsinkaye ya zama silar farkawar dukkanin masu ruwa da tsaki daga barci: Domin har sai Kano ta guji siyasar biyayya ta makanta da tumasanci, sannan makomarta za ta ƴantu daga hannun masu son zuciya, waɗanda ake ɗauka a matsayin gumakan siyasa.

Allah Ya bamu hikima, juriya da kuma tsawon rai mai amfani.

Advertisement

 

 

✍ Ibrahim Ishaq (Ɗan’uwa Rano)

Email: _danuwarano@gmail.com_

Advertisement

Telephone: _+2348056479966_

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *