Connect with us

News

Bayan Samun Ruwan Sama Mai Ƙarfi, Gwamnatin Kano Ta Fitar Da Sabon Gargadi Ga Jama’a

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargaɗi ga al’umma da su guji zubar da shara da kuma yin gine-gine a kan magudanan ruwa, tana mai cewa irin waɗannan dabi’u na iya jawo ambaliyar da ke barazana ga rayuka da dukiyoyi.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya fitar da wannan sanarwa ne a ranar Juma’a, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a yammacin Alhamis, wanda ya haddasa ambaliyar ruwa a wurare daban-daban na birnin Kano.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Sun Goyi Bayan Tsarin Mai Da Rubuta Jarabawar WAEC Ta Komfuta

Hashim ya ce ambaliyar ta nuna tasirin sauyin yanayi a muhalli, inda ya ce ba Kano kaɗai abin ya shafa ba, har ma da wasu birane a Najeriya kamar Legas, Abuja da Port Harcourt, da ma ƙasashen Turai da Amurka.

A cewarsa, gwamnatin Kano na ci gaba da ɗaukar matakai don rage barazanar ambaliyar ruwa, ciki har da share manyan magudanan ruwa da gyaran hanyoyin da ke toshewa.

Advertisement

Kwamishinan ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kare muhalli tare da tabbatar da cewa rayuka da dukiyoyin jama’a sun samu kariya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending