Politics
Duk Gwamnonin Arewa Yayansu Suke Gina Wa, Ba Arewa Bace A Gabansu — Adnan Mukhtar
Shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa, Adnan Mukhtar Tudun Wada, ya soki gwamnonin Arewacin Najeriya da cewa yawancinsu ba su sanya ci gaban Arewa a gaba, illa dai ‘ya’yansu da bukatunsu na kashin kai.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Tudun Wada ya bayyana cewa yawancin gwamnonin Arewa sun fi karkata wajen ginawa Yayansu rayuwa mai Kyau
Masana na nuni da cewa yan siyasa na tura ‘ya’yansu zuwa manyan makarantu a kasashen waje, maimakon su zuba jari wajen gyara makarantun cikin gida domin al’ummar da suka zabe su.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Makaniken Da Ya Sace Motar Abokiyar Cinikiyyarsa A Kano
Haka zalika lamarin ya tabbatar da cewa shugabannin Arewa sun manta da nauyin da ke wuyansu wajen inganta ilimi, kiwon lafiya da kuma rage radadin talauci da ke damun yankin.
“Abin takaici ne yadda Arewa ke ta fama da jahilci da talauci, amma shugabanninmu sun fi mayar da hankali wajen inganta rayuwar iyalansu maimakon ci gaban jama’a gaba ɗaya,” in ji Masana.
Wannan furuci ya tayar da muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin kalamansa gaskiya ne, yayin da wasu kuma suka ce an yi amfani da kalamai masu tsauri.
Sai dai Tudun Wada ya jaddada cewa lokaci ya yi da shugabannin Arewa za su dawo da kishin yankin, ba wai su yi wa kansu da ‘ya’yansu hidima
kawai ba.
