Interview
Matasa Sun Samar Da Kungiya Da Zata Kawo Sauyi Wajen Magance Matsalolin Fadan Daba Da Sace Sace A Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu matasa sun bude Sabuwar kungiyar mai suna Hasken Al’umma Foundation wacce zata kawo sauyi da kuma magance matsalolin fadan daba shaye shaye da sace sace daya adddabi Al’ummar jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa an kafa kungiyar ne don ta taimakawa wajen taimakon kai da kai domin shawo kan matsalalolin da akasarin jama’ar Unguwannin ke ciki.
A zantawarshi da Jaridar INDA RANKA mataimakin shugaban kungiyar mai Suna Shehu Nata’ala ya ce an samar da Kungiyar ne domin ceton mazauna jama’ar gari musamman ma Unguwar Dorayi da sace sace da kuma fadan daba yafi kamari.
Nata’ala ya ce bawai iya matsalolin da suka lissafa tun daga farkon bane suke kawo cikas ga jama’a kawai ,akwai matsaloli da dama ciki kuwa harda rashin ingantaccen samuwar Ilimi ga wasu daga cikin matasa.
Ya ce munsani cewar Ilimi shine gaba da komai a rayuwa kuma rashinsa yana iya kawowa kowacce Al’umma cikas a rayuwa .
A dan hakane kungiyar ta dukufa wajen kawu sauye sauye masu Inganci ta hanyar zaburar da matasan tare da kara nuna musu hanyoyin da zasu kawowa rayuwarsu cigaba mai dorewa ta yaddda zasu taimakawa kansu ya Iyalansu. Inji Nata’ala.
Nata’ala ya Kara da cewa akwai bukatar hadin kai wajen inganta ayyukan wannnan kungiyar ta fuskar bada hadin kai da jama’ar gari domin rashin hakan zai iyayin tasiri wajen kara bunkasar ayyukan da ba daidaiba.
Muddin anason cimmman nasara Tom sai jama’a a sun bada hadin kai domin a gudu tare a tsira tare.
Haka zalika kungiyar tayi kira da gwamnatin da masu hannu da shunni wajen taimakon kungiyar a kowanne lokacin domin dorewar ayyukan nata