News
TCN Ya Samar Da Sabbin Taransfoma A Legas Don Ƙara Inganta Hasken Wutar lantarki A Jihar
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa ya karɓi karin sabbin transfomar wutar lantarki guda bakwai don ƙara samar da wutar lantarki a jihar Legas.
Cikin wata sanarwa da Babban Manajan Hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya fitar, ya ce sabbin transfoma za su ƙara wa kamfanin mallakar Gwamnati da samar wutar lantarki inganta hasken wutar lantarki a jihar.
Sarkin Kano Muhammad Sunusi Ya Fito Domin Jagorantar Zaman Fada
“An kawo sabbin transfoma guda bakwai da ke da ƙarfin daga 60MVA zuwa 100MVA tare da kayan haɗin su zuwa tashar wutar lantarki ta Akangba 330/132kV.
“Wadannan transfoma ta haɗin gwiwa ce tsakanin TCN da Bankin Duniya kuma za a raba su zuwa tashoshin wutar lantarki ta Alausa 132/33kV, Akoka 132/33kV, Maryland 132/33kV, Itire 132/33kV, da Amuwo 132/33kV,” in ji TCN.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa kowacce daga cikin tashoshin da aka ambata za ta samu transfoma ɗaya, yayin da tashar Akoka 132/33kV da tashar Amuwo 132/33kV za su samu transfoma biyu kowanne.
“Da zarar an hadasu, transfoman za su haɓaka ƙarfin smar da wutar lantarki sosai,” in ji Mbah.
Da wannan ci gaban, ana sa ran jihohin Legas da Ogun za su samu ingantacciyar wutar lantarki
Najeriya na fama da gagarumin ƙarancin wutar lantarki ga mutanen kasar miliyan 200.
