Connect with us

News

NSCDC Ta Sallami Jami’an Sa-kai Biyar A Kano

Published

on

1780401369163 (1)

Rundunar Tsaro ta Sibil Difens ta Kasa (NSCDC) reshen Jihar Kano ta sallami jami’an sa-kai guda biyar daga aiki bisa laifin rashin da’a, rashin ƙwarewa da kuma karya ƙa’idojin aikin rundunar.

‎Kwamandan NSCDC na Jihar Kano, Muhammad Hassan Agalama, ne ya amince da matakin sallamar jami’an bayan binciken cikin gida ya tabbatar da cewa sun aikata laifukan da suka saɓa wa dokoki da ƙa’idojin rundunar.

Advertisement

2027: Labour Party Na Kokarin Zama Muryar Talakawan Najeriya

‎Jami’an da aka sallama sun haɗa da Yakubu Mubarak Yusuf, Isma’il Muhammad, Adamu Auwalu, Abdulrazaq Suleiman da kuma Ahmad Sarki.

Advertisement

‎A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar a jihar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an kwace dukkan kayan aiki da katunan shaidar aiki da ke hannun jami’an da aka sallama.

‎Sanarwar ta ce rundunar ta umarci dukkan sassa da ofisoshinta da ke faɗin jihar da kada su sake amincewa da mutanen a matsayin jami’an NSCDC ko ba su damar gudanar da wani aiki a madadin rundunar.

Advertisement

‎NSCDC ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin da’a ko halayen da za su iya bata mata suna ba, tana mai cewa duk wanda aka samu da irin waɗannan laifuka zai fuskanci hukuncin da ya dace ba tare da nuna son kai ba.

‎“Matakin da aka ɗauka ya nuna ƙudirin rundunar na tabbatar da bin doka, kiyaye ƙa’idojin aiki da kuma kare martabar hukumar,” in ji sanarwar.

Advertisement

‎Biyu daga cikin jami’an da abin ya shafa sun shaida wa manema labarai cewa sun amince da hukuncin da aka yanke musu, tare da cewa sun karɓi abin da ya faru a matsayin ƙaddara.

‎Rundunar ta kuma yi gargaɗi ga waɗanda aka sallama da kada su ci gaba da amfani da sunanta ko gabatar da kansu a matsayin jami’anta, tana mai cewa duk wanda aka samu da hakan zai fuskanci matakin doka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending