News
Amarya Ta Hallaka Uwargida Kan Takaddamar Rabon Naman Sallah
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wata amarya bisa zargin kashe uwargidan mijinta bayan wata takaddama da ake zargin ta samo asali daga rabon naman Sallah ta rikide zuwa tashin hankali a unguwar Gwargwaje da ke Zariya.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa matar da ake zargi ta soka wa uwargidanta, Amina Maharazu, wuƙa a Unguwar Madachi B da ke yankin Gwargwaje.
NSCDC Ta Sallami Jami’an Sa-kai Biyar A Kano
A cewarsa, bayan samun rahoton aukuwar lamarin daga mai unguwa, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin da gaggawa, inda suka tarar da matar cikin jini tana fama da munanan raunuka.
“An yi ƙoƙarin kai ta asibiti domin ceto rayuwarta, sai dai ta rasu kafin isa asibitin,” in ji DSP Hassan.
Ya bayyana cewa an kama wadda ake zargi kuma an miƙa ta zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike, kafin a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kakakin rundunar ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya yaba wa jami’an yankin Dan Magaji bisa saurin ɗaukar mataki da suka yi bayan samun rahoton lamarin.
Da yake bayyana alhininsa kan abin da ya faru, mijin matan biyu, Salisu Haruna, ya ce marigayiyar ce ta taimaka wajen haɗa aurensa da amaryar da ake zargi.
“Wannan babban rashi ne a gare mu. Ban taɓa tsammanin al’amura za su kai ga wannan mummunan ƙarshe ba,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Mai Unguwar Madachi B, Yamusa Sani Sarkin Fada, ya ce an sanar da shi faruwar lamarin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 30 ga watan Mayu.
“Da aka sanar da ni cewa an samu rikici tsakanin matan gidan kuma an soka wa ɗaya daga cikinsu wuƙa, nan take na tuntubi DPO na Dan Magaji domin ɗaukar matakin gaggawa,” in ji shi.
Majiyoyi daga unguwar sun shaida cewa rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan rabon naman Sallah, inda ake zargin amaryar ta nuna rashin jin daɗi bayan ta yi zargin cewa an fifita ’ya’yan uwargidan a kan ɗanta wajen rabon naman.
Wasu maƙwabta sun kuma bayyana cewa tun kafin faruwar lamarin ana samun saɓani a tsakanin matan gidan, musamman idan yara suka samu rashin jituwa. Sai dai sun ce marigayiyar ta shahara da haƙuri da son zaman lafiya.
Marigayiyar ta rasu ta bar ’ya’ya takwas da jikoki da dama, yayin da rahotanni suka nuna cewa ta riga ta aurar da biyu daga cikin ’ya’yanta kafin rasuwarta.
