News
2027: Labour Party Na Kokarin Zama Muryar Talakawan Najeriya
A yau, mutane da dama na kallon Jam’iyyar Labour Party a matsayin wata jam’iyya ta siyasa da wasu ’yan siyasa suka yi amfani da ita wajen samun farin jini ko cimma burinsu na siyasa. Sai dai idan aka yi nazari kan tarihinta, za a fahimci cewa asalin jam’iyyar ya sha bamban da yadda ake kallonta a yanzu.
Labour Party ba ta samo asali daga tattaunawar masu ruwa da tsaki ko kuma yarjejeniyar manyan ’yan siyasa ba. A maimakon haka, ta samo tushe ne daga gwagwarmayar ma’aikatan Najeriya. A shekarar 2002 ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta kafa Jam’iyyar Party for Social Democracy (PSD), wadda daga bisani ta rikide zuwa Labour Party.
An kafa jam’iyyar ne domin samar da wata kafa ta siyasa da za ta kare muradun ma’aikata da talakawa, tare da gina manufofinta a kan adalci, daidaito, hadin kai da kare mutuncin dan Adam.
Taken jam’iyyar na “Forward Ever” ba wata kalma ce ta ado ba, illa wata alama ce ta ci gaba da gwagwarmayar neman ingantacciyar rayuwa ga ’yan kasa.
Daya daga cikin muhimman manufofin Labour Party shi ne tabbatar da cewa talakan Najeriya yana iya biyan bukatunsa na yau da kullum cikin sauki. Jam’iyyar na da ra’ayin cewa bai kamata ma’aikata su ci gaba da rayuwa cikin kunci a kasar da Allah Ya albarkace ta da dimbin albarkatun kasa da na dan Adam ba.
Ba kamar wasu jam’iyyun siyasa da ke fitowa ne kawai lokacin zabe ba, Labour Party na da wata kafar da ta bazu a fadin kasar nan ta hanyar kungiyoyin kwadago. Tare da goyon bayan NLC da TUC, jam’iyyar na da alaka da kungiyoyin ma’aikata a dukkan kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Wannan tsarin ya ba ta damar isa ga al’umma cikin sauki, tare da karfafa wayar da kai da tattara magoya baya a sassa daban-daban na kasar.
Sai dai duk da wannan fa’ida, jam’iyyar ta fuskanci kalubale masu yawa a shekarun baya, ciki har da rikice-rikicen cikin gida, takaddamar shugabanci da rabuwar kai, wadanda suka girgiza amincewar wasu daga cikin magoya bayanta.
Duk da haka, siyasa hanya ce ta sabuntawa. Bayyanar shugabancin Sanata Nenadi Usman da kokarin sake farfado da jam’iyyar sun bude wata sabuwar dama ga Labour Party domin sake tsara tafiyarta.
A yanzu haka, jam’iyyar na da nauyin sake gina amincewar jama’a, karfafa dimokuradiyya a cikinta da kuma dawo da martabarta a matsayin jam’iyyar da ke wakiltar muradun talakawa.
Haɗuwar gogaggun ’yan siyasa da jiga-jigan kungiyar kwadago a karkashin jam’iyyar na iya zama wata hanya ta samar da daidaito da karfin da ake bukata wajen tunkarar kalubalen da ke gaba.
Bayan nazarin halin da Najeriya ke ciki da kuma gogewar da aka samu a harkokin kwadago, abu daya ya bayyana karara: sadaukarwa ga tafarkin kwadago ba shiga siyasa kawai ba ne, wata akida ce da ta samo asali daga gwagwarmayar rayuwa da kalubalen da talakawa ke fuskanta.
Haka kuma, ba za a yi magana kan Labour Party ba tare da ambaton Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ba. A matsayinsa na gwamnan jam’iyyar daya tilo, ya ci gaba da tsayawa tare da jam’iyyar duk da sauye-sauyen siyasa da matsin lamba daga bangarori daban-daban.
A cewar marubucin, tarihi kan fi tunawa da wadanda suka tsaya kan akidarsu fiye da wadanda suka bi ra’ayin jama’a saboda wata bukata ta siyasa.
A lokacin da matsalolin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da karuwar gibin talauci ke ci gaba da addabar kasar nan, Najeriya na bukatar shugabanci mai kwarewa, tausayi da manufofin da suka ginu kan adalci.
Saboda haka, ya kamata ’yan Najeriya su yi nazari mai zurfi kan irin jam’iyyun da suke mara wa baya, tare da bai wa dama ga wata kafa da aka gina daga gwagwarmaya, hadin kai da muradun ma’aikata.
A cewar marubucin, bai kamata Labour Party ta takaita burinta ga nasarar zaben 2027 kawai ba, ya kamata ta zama wata alama ta fata ga ’yan Najeriya masu neman adalci, rikon amana da ci gaban tattalin arziki.
Domin kuwa, kamar yadda karin magana ke cewa, “mai takalmi shi ne ya fi sanin inda yake matse shi.”
Najeriya na bukatar shugabanci nagari. Ma’aikata na bukatar mutunci. ’Yan kasa kuma na bukatar gwamnati mai sauraro da amsa bukatunsu.
Lokaci ya yi da za a sake tsara tafiya, a hada kai, a wayar da kai tare da ci gaba da tafiya karkashin taken:
“Forward Ever, Backward Never” domin gina Najeriya mai adalci, wadata da ci gaba.
– Kwamared Abbas Ibrahim ya rubuto daga Jihar Kano.
