News
Mutum Uku Sun Fada Rijiya A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce ta ceto mutum uku da suka fada cikin Rijiya a Kananan Hukumomin Kumbotso da Warawa a ranar Juma’a.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 29 ga Mayu, 2026.
2027: Ba Zan Taba Juya Wa Kwankwaso Baya Ba — Goro
A cewar sanarwar, cibiyar karbar kiraye-kirayen gaggawa ta hukumar ta samu rahotannin aukuwar lamarin daga wurare biyu tsakanin karfe 7:06 na safe zuwa 9:40 na safe.
Rahoton farko ya nuna cewa wani mutum da ba a tantance ko wanene ba mai kimanin shekaru 40 ya fada cikin wata rijiya a yankin Semegu da ke kusa da kamfanin El-Sadeeq Bread a Karamar Hukumar Kumbotso.
Jami’in ya ce, “Jami’an kashe gobara daga babbar sakatariyar hukumar sun ceto shi yana sume, inda suka mika shi ga Jami’in Binciken Manyan Laifuka (DCO) na Rundunar ‘Yan sandan Panshekara, Salisu Salihu domin ci gaba da bincike.”
A wani lamari makamancin haka kuma, jami’an hukumar sun ceto wata mata mai suna Maimuna Shitu mai shekaru 32 tare da danta Harisu Muntari mai watanni 18 bayan sun fada cikin wata rijiya a kauyen Madarin Taba da ke Karamar Hukumar Warawa.
Rahotanni sun nuna cewa mahaifin matar, Muhammad Shitu, ya bayyana cewa ’yarsa na fama da matsalar tabin hankali.
An ceto duka mutanen biyu suna sume, kuma an mika su ga Mai Garin yankin, Yusuf Surajo, da kuma mahaifin matar Muhammad Shitu,” in ji Jami’in Hulda da Jama’an.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
