News
Gwamnoni Na Duba Yiwuwar Karin Mafi Karancin Albashi Zuwa Naira 100,000 — Gwamnan Kwara
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce gwamnonin Jihohi na duba yiwuwar biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 100,000 domin rage radadin halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar.
AbdulRazaq ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya fitar a shafinsa na Facebook a yau Asabar, inda ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki, tsadar rayuwa, da kuma karancin kudi ga ma’aikatan Najeriya ya sanya su ka duba yuwuwar karin.
2027: Ba Zan Taba Juya Wa Kwankwaso Baya Ba — Goro
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi suna tattaunawa da Gwamnatocin Tarayya da kuma kungiyoyin kwadago domin cimma matsaya kan tsarin albashin da zai inganta jindadin ma’aikata.
Acewarsa gwamnonin Jihohin sun amince akwai bukatar gaggawa ta inganta jin dadin ma’aikata dangane da yanayin tattalin arziki da Ƙasar ke fuskanta.
Shugaban kungiyar ya ce Manufar ita ce inganta rayuwar ma’aikata, ba tare da an durkusar da asusun jihohi ba, ta yadda jihohi za su iya ci gaba da gina ayyukan more rayuwa da gudanar da ayyukan gwamnati.
A halin yanzu dai mafi karancin albashi a Najeriya naira 70,000 ne a kowane wata.
Sai dai wasu rahotanni sun ce jihohi da dama da su ka hada da Legas da Ribas da kuma Imo suna biyan mafi karancin albashin fiye da haka a wani mataki na tallafawa ma’aikata.
Ana sa ran shirin samar da mafi karancin albashi na Naira 100,000 zai kara karfafa tattaunawa a kasar kan batun albashi, hauhawar farashin kayayyaki, da kuma sake fasalin tattalin arziki yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan abinci, tsadar sufuri da sauran al’amuran da su ka shafi rayuwa.
A gefe guda kuma Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC na ci gaba da matsa lamba domin sake duba albashin ma’aikatan, inda su ka jaddada cewa ma’aikata sun cancanci albashin da zai iya daukar nauyin rayuwarsu ta yau da kullum daidai da yanayin tsadar rayuwa, maimakon albashin da za su ci gaba da rayuwa cikin wahala.
