News
Sarkin Kano Muhammad Sunusi Ya Fito Domin Jagorantar Zaman Fada
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II ya fito domin fara jagorantar zaman fada na Yau Juma’a a fadar Sarki da ke Kofar Kudu.
Wanann na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun mamaye gidan Sarkin Kano, tare da hana Sarki Muhammadu Sunusi fita don tafiya masarautar Bichi.
DA ƊUMI-ƊUMI: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Fadar Sarkin Kano Sun Hana Shiga Ko Fita
Da fari Sarki Sanusi ya shirya jagorantar tawaga zuwa raka sabon hakimin Bichi zuwa fadarsa, tare da gudanar da wasu aika-aikace.
To amma tuni dubban jamian tsaro suka mamaye fadar Sarki ta Kofar Kudu don hana Sarkin Fita zuwa ziyarar da ya shirya gudanarwa.
Kawo yanzu haka Sarkin ya zauna domin fara jagorantar zaman fada na Yau Juma’a kamar yadda ya saba gudanarwa.
PREMIER RADIYO ta ruwaito cewa babu tabbacin suwa ne suka bayar da umarnin girke jamian tsaro a fadar Sarki da ke Kofar Kudu, amma zargi na alamta bangaren masu hamayya da gwamnatin Kano ne ke da hannu kan batun.
