News
Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato
Aƙalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu, ciki har da masu yawon Sallah bakwai, bayan wasu mahara sun kai hari ƙauyen Dangulbi da ke Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa maharan, waɗanda suka zo a kan babura masu yawa ɗauke da makamai, sun mamaye ƙauyen da safiyar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe tare da wawashe dukiyoyin jama’a.
Mutum Ɗaya Ya Mutu, Uku Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Adaidaita Sahu
Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce maharan sun shiga ƙauyen tsakanin ƙarfe 10 zuwa 11 na safe, kuma nan take suka fara harbi, abin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai baƙi bakwai da suka je ƙauyen domin gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu. Biyar daga cikinsu sun fito ne daga ƙauyen Adarawa da ke Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara, yayin da sauran biyun suka fito daga Gidan Gambo da ke Ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato.
Majiyar ta ce ana zargin maharan sun fito ne daga yankin Bagega da ke Ƙaramar Hukumar Anka a Jihar Zamfara, inda suka bi ta Barayar Zaki kafin su yada zango a ƙauyen Gizazza, daga bisani suka kai harin da safiyar Lahadi.
A cewarsa, maharan sun shafe sa’o’i da dama a cikin ƙauyen bayan harin, lamarin da ya hana jama’a gudanar da jana’izar mamatan har zuwa bayan ficewarsu.
“Sai bayan misalin ƙarfe bakwai na yamma suka bar ƙauyen. Daga nan ne mutane suka dawo, kuma aka yi jana’izar mamatan da misalin ƙarfe 9:30 na dare,” in ji majiyar.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma fasa shaguna kusan 20 tare da wawashe kayayyaki da dama. Hakan ya sa wasu mazauna yankin tserewa zuwa yankunan Gummi, Shagari, Tureta da Bukkuyum domin neman mafaka.
Bayan barin Dangulbi, an ce maharan sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka da ke maƙwabtaka da yankin, ciki har da Kukoki da Birnin Magaji, inda suka yi garkuwa da wasu mutane.
Sai dai wata majiya ta ce mutanen da aka sace sun samu damar tserewa bayan wata iska mai ƙarfi da ruwan sama da suka afku a daren Lahadi, lamarin da ya haddasa ruɗani a tsakanin maharan.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun sake kai farmaki wasu ƙauyuka a safiyar Litinin, inda suka ci gaba da harbe-harbe da tayar da hankalin jama’a.
Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Sakkwato da su ƙara ɗaukar matakan tsaro domin dakile hare-haren da suka ce suna ƙara tsananta a yankin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, ya tabbatar da samun rahoton harin, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin shawo kan lamarin.
Mahara Sun Wawashe Shaguna, Sun Tilasta Wa Jama’a Tserewa
Baya ga asarar rayuka, harin ya jawo asarar dukiyoyi masu yawa bayan maharan sun fasa tare da wawashe shaguna da dama a ƙauyen. Mazauna yankin sun ce lamarin ya haddasa ƙaura ta gaggawa, inda iyalai da dama suka bar gidajensu saboda fargabar sake kai hare-hare.
Masu ruwa da tsaki a yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙarfafa ayyukansu a yankunan karkara da ke fama da hare-haren mahara domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
