News
Mutum Ɗaya Ya Mutu, Uku Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Adaidaita Sahu
Wani mutum ya rasa ransa, yayin da wasu mutum uku suka jikkata a wani hatsarin Adaidaita Sahu da ya afku a titin Haske da ke kusa da Lamingo Golf Club a birnin Jos na Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin lokacin da wasu Adaidaita Sahu biyu suka yi mummunan karo da juna.
An Fizgo Shugaban Jam’iyyar NDC Daga Kan Babur Yayin Da Aka Kona Fastocin Obi Da Kwankwaso A Kano
Wani ganau mai suna Joseph Haruna ya shaida cewa hatsarin ya samo asali ne bayan direban ɗaya daga cikin Adaidaita Sahu ya yi ƙoƙarin kauce wa wani rami da ke tsakiyar hanya, amma ya kasa shawo kan abin hawansa.
“A yayin da yake ƙoƙarin kauce wa ramin ne ya rasa iko da Adaidaita Sahu, sannan ya kutsa cikin wata Adaidaita Sahu da ke tahowa daga gaba,” in ji shi.
Haruna ya ce ƙarfin karon ya yi muni matuƙa, inda wani fasinja ya mutu nan take a wurin, yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka daban-daban.
Rahotanni sun nuna cewa jama’a da jami’an agajin gaggawa sun yi saurin kai waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti domin samun kulawar likitoci.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana hatsarin a matsayin abin takaici, yana mai kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ramukan da suka lalata titin.
Ya ce matsalar lalacewar hanyar na ci gaba da jefa masu ababen hawa da masu amfani da Adaidaita Sahu cikin haɗari a kullum.
Hatsarin ya haddasa cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci a yankin, yayin da mutane da dama suka taru domin ganin yadda lamarin ya faru.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa da na agajin gaggawa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan hatsarin ba.
