Connect with us

Interview

Masarautar Daura Ta Nada Sarautu Ga Wadanda Suka Hidimta Wa AL-QUR’ANI Da Almajirrai

Published

on

IMG 20250205 WA0021
Spread the love

Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal, Sokoto

 

Masarautar Daura da ke jihar Katsina ta nada sarautu biyu ga wasu bayin Allah da suka yi fafutuka wajen tabbatar da hakkokin almajirai da makarantun tsangaya.

Advertisement

Tsohon dan majalisar tarayya daga Sokoto, Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale, an ba shi sarautar Barden Makarantun Tsangaya da Makarantun Allo na Kasar Hausa. Haka kuma, Hajiya Aisha Jibril Dikku an nada ta matsayin Sarauniyar Tsangayu da Makarantun Allo.

Shugaba Tinubu Ya Nemi A Kara Yawan Kasafin Kudin 2025 

Nadin sarautar ya gudana ne tare da wasu nade-nade a fadarsa Mai Martaba Sarkin Daura, Alh. Dr. Umar Farouk Umar CON. A yayin bikin, Sarkin Daura ya bayyana cewa:

“Duk inda Tsangayun Makarantun Allo suke a ƙasar Hausa da kuma jihohi goma sha tara (19) na Arewacin Najeriya, mun umurce ka da ka wakilce mu.”

Advertisement

An nada wadannan bayin Allah ne domin su taka rawar gani wajen ci gaba da kare hakkokin almajirai. A lokacin da suke majalisar dokoki, sun yi aiki tukuru har aka sanya dokar kare hakkin almajirai da yaran da ba su karatu hannu. Wannan dokar ce ta ba da damar kafa hukuma mai kula da inganta karatun tsangaya da almajirai a Najeriya, wadda ake cin moriyarta a yau.

Sabon Barden Makarantun Tsangaya da Makarantun Allo, Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale, ya nuna matukar godiyarsa ga Masarautar Daura bisa wannan girma da aka yi masa. Ya kuma godewa duk wadanda suka halarta daga ciki da wajen Daura, har ma da makwabtan kasashe kamar Maradi a Nijar da Senegal.

Bayan kammala nadin sarautar, an yi hawan daba tare da kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *