News
Shugaba Tinubu Ya Nemi A Kara Yawan Kasafin Kudin 2025
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nemi a kara yawan kasafin kudin 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.
Buƙatar hakan na kunshe ne cikin wata wasika da shugaban ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kuma aka karanta zauren majalisar a zamanta na Laraba.
EL-RUFAI YA SHIGA RIKICIN RIBADU / NAJA’ATU : Ribadu Na Fama Da Matsananciyar Cutar Mantuwa
Aidan za’a iyab tunawa a ranar 18 ga Disamba, 2024, Shugaban ƙasar ya gabatar da ƙudurin kasafin kudi na Naira tiriliyan 49.7 ga hadakar zauren Majalisar Dokoki.
Sai dai a cikin wasikar da ya aike wa Majalisar, Shugaban ya bayyana cewa ƙarin karin kudaden shiga na Naira tiriliyan 1.4 da aka samu daga Hukumar tara Haraji ta Kasa (FIRS), da kuma Naira tiriliyan 1.2 da Hukumar Kwastam ta ta samu, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka samar ya sanya neman karin yawan kasafin kudin na bana.
Bayan karanta wasikar Shugaban ƙasar, Shugaban Majalisar Dattawa ya umarci Kwamitin Kula da Kasafin Kudi da su gaggauta duba bukatar.
Ya kuma bayyana cewa za a kammala nazarin kasafin kudin kafin ƙarshen watan Fabrairu, da kuma amincewa da shi.
