News
Shugaba Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Kore Wasu Kwamishinonin Zaɓe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A yau Laraba, Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin korar wasu kwamishinonin zabe (RECs) na jihohin Abia, Adamawa, da Sokoto da aka dakatar.
Wannan bukata tana kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban kasa ya aike wa shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya karanta a zauren majalisar.
Masarautar Daura Ta Nada Sarautu Ga Wadanda Suka Hidimta Wa AL-QUR’ANI Da Almajirrai
Kwamishinonin zaben da aka dakatar da kuma Tinubu ke neman sallamarsu sun hada da:
Ike Uzochukwu (Abia)
Hudu Yunusa-Ari (Adamawa)
Nura Ali (Sokoto)
Ana zargin wadannan kwamishinoni da aikata rashin da’a da kuma saba ka’idojin aiki a lokacin babban zaben 2023.
Shugaban kasa ya bukaci Majalisar Dattawa da ta amince da sallamar su domin tabbatar da ingantaccen tsarin zabe da rikon amana a harkar gudanar da zabuka a Najeriya.
