Connect with us

News

An Kai Karar Maigari, Mai Unguwa, Dan Sanda da Limami Bisa Zargin Karɓe Kuɗaɗen Matashi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ana tuhumar wasu manyan mutanen gari a ƙaramar hukumar Bagwai da haɗa kai wajen karɓe kuɗaɗen wani matashi Bafulatani da zummar yi masa tara, amma daga bisani suka raba kudin a tsakaninsu.

Mutanen da ake zargi sun haɗa da Maigari, Mai Unguwa, wani ɗan sanda da Limami, waɗanda suka gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Rijiyar Lemo, Kano.

Dillalan Man Fetur A Fadin Kasar Sun Koma Hulda Da Matatar Dangote Bayam Sun Fara Yanke Alaka Da NNPC

Wanda abin ya shafa, matashi Umar Musa, ya shaida wa wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki cewa an karɓi N130,000 daga gare shi bisa hujjar cewa ya deɓi hatsin ƙaninsa. Amma daga bisani, ƙanin nasa ya bayyana cewa bai damu da ɗiban hatsin ba.

Lamarin na cigaba da ɗaukar hankali, yayin da jama’a ke jiran hukuncin da kotu za ta yanke a kan waɗanda ake zargi da wannan aika-aika.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending