News
Ƙudirin Cin Tarar N25,000 Kan Fitsari da Tofar da Yawu a Titi Na Tayar Da Ƙura A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar da ke haramta yin fitsari, ba-haya, zubar da shara, da tofar da yawu ko majina a tituna, ƙarƙashin gadoji, gine-ginen gwamnati, da wuraren taruwar jama’a. Duk wanda aka kama yana aikata waɗannan abubuwa zai fuskanci tarar naira 25,000 ko kuma hukuncin ɗaurin gidan yari idan ya kasa biyan tarar.
Majalisar ta zartar da wannan ƙudiri a ranar Litinin, inda yanzu aka miƙa shi ga gwamnan jihar domin sanya hannu kafin ya zama doka mai cikakken ƙarfi.
Dan majalisa Abdulmajid Isa Umar Mairigar Fata, mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale, ya bayyana cewa wannan ƙudiri wani ɓangare ne na shirin gyara da kawata birnin Kano. Sai dai, jama’a sun fi mayar da hankali kan abin da ya shafi tofar da yawu da majina, tare da bayyana ra’ayoyi mabambanta.
Jihar Kano na fama da matsalar zubar da shara da bahaya a bainar jama’a, abin da ke hana tsafta da kuma haifar da rashin ɗa’a. Sai dai, wasu masu sharhi sun yi nuni da cewa kafin aiwatar da wannan doka, ya dace gwamnati ta samar da isassun wuraren zubar da shara da bahaya domin bai wa al’umma sauƙi.
Yanzu dai ana jiran matakin da gwamna zai ɗauka game da ƙudirin, yayin da al’ummar Kano ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan batun.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
