News
Gobara Mai Muni Ta Lalata Kauyen Zago A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata mummunar gobara ta afkawa kauyen Zago da ke karamar hukumar Dambatta a jihar Kano a ranar Laraba, inda ta haddasa konewar gidaje, dabbobi, da rumbunan abinci.
Wani ganau, Laminu Sani, ya tabbatar wa AREWA RADIO da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba.
A cewarsa, gobarar ta fara ne bayan karfe 9 na safiyar Laraba kuma ta ci gaba har zuwa karfe 4 na yamma, sakamakon wahalar da aka fuskanta wajen samun ruwa da kuma matsalar hanya da ta hana jami’an kashe gobara isa wurin da wuri.
Dagacin kauyen, Yunusa Isma’il, shi ma ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da yin kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta kai dauki ga mutanen da gobarar ta shafa.
Har yanzu, ba a tantance yawan asarar da aka tafka ba, sai dai jama’ar kauyen na ci gaba da kokarin farfadowa daga wannan ibtila’i.
