News
Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban NYSC da Wasu Mutane
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar masu hidimtawa kasa (NYSC), Manjo Janar Mahraz Tsiga (mai ritaya), tare da wasu mutanen kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace mutanen ne a tsakar daren Laraba, duk da cewa hukumomi har yanzu ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin.
Wata majiya ta shaidawa Prime Time cewa, tabbas tsohon shugaban hukumar NYSC yana cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Tsiga.
Har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto, babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Katsina ko rundunar ‘yan sanda dangane da sace mutanen.
Advertisements
